Hausa News: Hajiya Aisha Buhari tayi abin kwarai

– Matar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta mamayi wasu Yara da ke Makarantar Katolika ta Kirista
– Uwargidan Shugaban Kasar ta yi alkawarin samawa Yaran Makarantar ilmi mai nagarta
– Matar Shugaban Kasan ta rabawa ‘Yan Makarantar kayan abinci
Hajiya Aisha Buhari tayi abin kwarai
Hajiya Aisha Buhari tayi abin kwarai
Matar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Buhari ta bada gudumuwar kayan abinci ga Yara kusan 300 da ba su da Gida wanda rikicin Boko Haram ya ritsa da su. Matar Shugaban Kasar dai ta bada wannan gudumuwa ne a Makarantar Katolika ta Paraxis.
Misis Paul Tallen, Tsohuwar Matainakiyar Gwamnan Jihar Plateau ta wakilci Matar Shugaban Kasar inda aka rabawa wadannan kayayyaki. Mai Makarantar, Mista Ben Onwudinjo ya tabbatar da wannan abin alheri daga Hajiya Aisha Buhari.
Hukumar Dillacin labarai na Kasa watau NAN tace Matar Shugaban Kasar tayi alkwarin samawa wadannan Dalibai na Makarantar Paraxis na Katolika ta Addinin Kirista nagartaccen Ilmi. Tuni ma dai har an sauyawa Makarantar suna zuwa Makarantar Hajiya Aisha Buhari.
A jiya kuma muka samu labarin Uwargidan Gwamnan Jihar Ekiti, Feyisetan Fayose ta nemi Ubangiji ya kare Mijin ta ya kuma tona asirin makiyan sa. Matar Gwamnan tace akwai masu rabar Mijin ta alhali kuma ba masoyan sa bane na hakika.

No comments

Powered by Blogger.