An kusa damke Shekau Inji wani Fasto

– Wani Malamin Addinin Kirista yace a shekarar nan za a kama Shekau
– Salon Yaki da Boko Haram ya hana a damke Shekau Inji Fadar Shugaban Kasa
– Mai magana da bakin Shugaban Kasa yace karshen Shekau din ya zo
An kusa damke Shekau Inji wani Fasto
An kusa damke Shekau Inji wani Fasto
Wani Babban Fasto a Kasar nan, Bishof Fomson ya bayyana irin abin da ya gano masu faruwa a shekarar nan. Faston yace a shekarar bana ne za a kama Shugaban Kungiyar Boko Haram dinnan, Abubakar Shekau.
Faston yace a shekarar nan abubuwa za su yi kyau a Najeriya. Ya kuma nemi mutanen Kasar su hada da addu’a. Faston yace Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai ba marada kunya a shekarar banan nan. A karshe ya dai nemi Jama’a su tuba daga zunaban su.
Femi Adesina, mai taimakawa Shugaban Kasar wajen yada labarai yace Yakin Boko Haram ba na taho-mu-gwabza bane, hakan ya hana a kama Shugaban Kungiyar Abubakar Shekau tuni. Yace amma karshen na sa fa ya zo a hannun Sojin Najeriya.
Kowane Fasto dai na irin na sa harsashen a sabuwar shekarar, kwanaki ma dai wani yace Shugaba Buharin zai mutu, wani takwaran na sa kuma yace zai shekaru takwas bisa mulki.

No comments

Powered by Blogger.