Sojoji sun kashe wasu yan kunar bakin wake 3, sun dakile hari na biyu a Adamawa cikin sa’oi 24

- Cikin kasa da sa’oi 24, sojin Najeriya sun dakile wani hari da kuma kashe yan kunar bakin wake uku a jihar Adamawa
- Shugaban karamar hukumar Madagali da kuma Badare Akintoye, kakakin bataliyan soji 28 a Mubi ya tabbatar da dakile hare-haren guda biyu
Sojoji sun kashe wasu yan kunar bakin wake 3, sun dakile hari na biyu a Adamawa cikin sa’oi 24
Sojoji sun kashe wasu yan kunar bakin wake 3, sun dakile hari na biyu a Adamawa cikin sa’oi 24
Sojojin Najeriya sun kashe yan kunar bakin wake mata a jihar Adamawa don kai wani hari a yankin area maso gabas a farkon shekara.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa an kashe yan kunar bakin waken a kauyen Bakin Dutse, a karamar hukumar Madagali dake jihar.
Am kama matan ne a kauyen dake tsawon kilomita biyar daga Gulak inda daruruwan mutane suka taru don cin kasuwa a hedkwatan karamar hukumar Madagali.
Kakakin sojin bataliya 28 a Mubi, Badare Akintoye ne ya tabbatar da al’amarin.
Wannan ne Karo na biyu da aka Kai hari a Madagali cikin sa’oi 24.
Ku tuna cewa a ranar Tamara 3 ga watan Janairu rundunar sojin sun dakile wani harin mayakan Boko Haram wadanda sukayi yunkurin kai hari a kauyen Dar, haka kuma a karamar hukumar Madagali.

No comments

Powered by Blogger.